Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa hadimansa umarni da su shirya tsawaita matakin kakaba wa Iran takunkumi mai tsauri ta hanyar ci gaba da toshe hanyoyin kasuwanci da jigilar kayayyaki zuwa da daga tashoshin jiragen ruwan kasar.
Rahotanni daga jaridar The Wall Street Journal sun bayyana cewa Trump ya zabi wannan hanya ne bayan tattaunawa da jami’an tsaro da na siyasa, inda ya ga cewa ci gaba da matsin tattalin arziki kan Iran ya fi sauki da karancin hadari idan aka kwatanta da sake kai farmakin soji ko kuma janyewa gaba daya daga rikicin.
A cewar jami’an Amurka, manufar wannan shiri ita ce kara raunana tattalin arzikin Iran musamman ta fuskar fitar da mai, wanda ke daya daga cikin manyan hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnatin Tehran.
Rahoton sununa Trump ya yi imanin cewa sake fara kai hare-haren bama-bamai kan Iran na iya haddasa babbar rikici a Gabas ta Tsakiya, yayin da janyewa daga rikicin kuma zai iya bai wa Iran damar kara karfi.
Saboda haka, gwamnatin Amurka na son ci gaba da amfani da dabarar killace Iran ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci domin rage tasirinta a yankin.
Tun a ranar 28 ga Fabrairu ne Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare hadin gwiwa kan wasu wurare a Iran, lamarin da ya sa Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan wuraren da ta kira muradun Amurka a yankin, musamman a wasu kasashen Gulf.
Wannan sabon mataki na toshe hanyoyin ruwa na nuna cewa Washington na kokarin amfani da matsin lamba na dogon lokaci domin tilasta Iran sauya manufofinta ba tare da fadawa cikin cikakken yakin kasa-da-kasa ba.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan tsari na iya kara dagula tattalin arzikin Iran, tare da yiwuwar kara tashin hankali a yankin idan Tehran ta dauki wasu matakan ramuwar gayya.
