Jami’ar Achievers University ta gano wata badakalar zargin damfarar kudin makaranta har Naira miliyan 457.5 bayan gudanar da binciken cikin gida kan biyan kudin dalibai a zangon karatu daban-daban.
Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Oyesoji Aremu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, inda ya ce an kammala binciken ne a ranar Juma’a.
A cewar jami’ar, ana zargin wata tsohuwar ma’aikaciyar sashen kudi da kutse cikin tsarin biyan kudin makarantar tare da karkatar da kudaden dalibai zuwa asusun ajiyarta na banki.
Jami’ar ta ce dalibai 320 sun biya jimillar N457,508,645 cikin asusun matar a zangon karatu na 2023/2024, 2024/2025 da 2025/2026, yayin da aka goge bayanansu a tsarin makarantar ba tare da kudin sun shiga asusun jami’ar ba.
Sanarwar ta bayyana cewa matar, wacce tsohuwar dalibar sashen Accounting ce kuma daga baya ta yi aiki a sashen bursary, ta yi murabus daga aiki a watan Afrilun 2025.
An kuma ce wasu dalibai sun fada tarkon biyan kudin ne bayan an yi musu alkawarin rangwamen kudin makaranta da kuma samun kwamitin anfani.
Binciken ya kuma gano cewa ma’aikata 11, dalibai 34 da wani mutum guda daga wajen jami’ar mai alaka da wani Federal Medical Centre ana zarginsu da taka rawa wajen jawo dalibai shiga tsarin damfarar.
Aremu ya ce daliban da abin ya shafa, ciki har da wadanda ake zargi da zama wakilai, za su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na dalibai domin bayyana rawar da suka taka da dalilin kauce wa hanyoyin biyan kudin makaranta na hukuma.
Ya kara da cewa ma’aikatan da ake zargi za su fuskanci kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikata, yayin da ake ci gaba da binciken ‘yan sanda kan babbar wacce ake zargi, kuma tana iya fuskantar shari’a.
Mukaddashin shugaban jami’ar ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da duba kudaden makaranta da tsofaffin dalibai suka biya cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya ce majalisar gudanarwar jami’ar ta amince da gudanar da binciken cikin gaskiya tare da sanar da al’umma duk wani ci gaba domin dakile yada op ojita-jita.
