Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS) reshen Arewacin ƙasar ta bukaci ‘yan Najeriya, musamman mazauna Arewa, da su guji siyasantar da sabon tsarin gyaran fitar da fasfo da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ke aiwatarwa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa gyaran tsarin wani shiri ne na zamani da ya shafi ƙasa baki ɗaya, ba wani mataki ba ne da aka ɗauka domin tauye haƙƙin wata shiyya.
Mataimakin Shugaban NANS mai kula da harkokin waje, Comrade Sadiq SK Zango, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa tsarin Passport Centralisation Programme an ƙirƙire shi ne domin cutar da jihohin Arewa.
A cewarsa, irin waɗannan zarge-zarge ƙarya ce da kuma yaɗa bayanan da ba su da tushe, waɗanda aka yi domin rikita al’umma.
Zango ya ce sauya aikin buga fasfo zuwa Cibiyar Central Personalisation Centre da ke Abuja ba ya nufin an dakatar da karɓar buƙatun fasfo ko fitar da su a ofisoshin hukumar da ke faɗin ƙasar ko kuma ofisoshin jakadancin Najeriya da ke ƙasashen waje.
Ya bayyana cewa wannan sauyi wani ɓangare ne na shirin inganta tsarin fitar da fasfo, ƙara tsaro, tabbatar da inganci da kuma saurin gudanar da ayyukan hukumar.
A cewarsa, binciken da NANS ta gudanar ya nuna cewa an tattara dukkan ayyukan buga fasfo da saka matakan tsaro a cibiyar zamani mai ƙarfin aiki da ke Abuja.
Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai ba da damar samar da fasfo cikin makonni biyu, tare da rage jinkiri, kawar da sa hannun mutane ba bisa ƙa’ida ba, ƙarfafa gaskiya da tabbatar da cewa dukkan fasfo na Najeriya suna da ingantattun matakan tsaro na zamani.
Zango ya kuma bukaci al’ummar Arewa da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa game da shirin, yana mai tabbatar da cewa gyaran tsarin zai samar da fasfon Najeriya mai inganci da karin kima a idon ƙasashen duniya.
