Gwamnatin Jihar Yobe tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Qatar Charity sun ƙaddamar da shirin ba da kulawar ido kyauta domin inganta lafiyar al’ummar jihar.
An ƙaddamar da shirin ne a Asibitin Kwararru na Jihar Yobe da ke Damaturu, inda zai gudana na tsawon kwanaki biyar.
Gwamna Mai Mala Buni, wanda mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana ya wakilta, ya ce shirin wata babbar nasara ce ta haɗin gwiwar gwamnatin jihar da Qatar Charity. Ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen dawo da gani ga masu fama da matsalolin ido, wanda hakan zai inganta rayuwarsu da damar samun ilimi da sana’a.
A cewarsa, shirin ya haɗa da duba ido kyauta, tiyatar cataract ba tare da biyan kuɗi ba, raba magunguna da kuma ba marasa lafiya tabarau kyauta bayan an yi musu gwaji da jinya.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da samar da ingantattun ayyukan lafiya, ciki har da shirye-shiryen dialysis kyauta, kula da lafiyar mata masu juna biyu da yara, da gina cibiyoyin lafiya a dukkan gundumomin jihar.
A nasa jawabin, Daraktan Qatar Charity a Najeriya, Assen Abu Al-Ashaeer, ya tabbatar da cewa gidauniyar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Yobe domin faɗaɗa ayyukan jin ƙai a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun yabawa gwamnatin jihar da Qatar Charity bisa wannan tallafi, suna mai cewa zai sauya rayuwar dubban mutane masu fama da matsalolin gani.
