Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, yana mai cewa yana alfahari da yadda ya tsaya tsayin daka wajen hana yunkurin wa’adi na uku da aka yi a lokacin gwamnatin Obasanjo.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce kalaman Obasanjo na baya-bayan nan ƙoƙari ne na karkatar da tarihin siyasar Najeriya.
Atiku ya ce tsayawarsa kan yunkurin wa’adi na uku ba saboda gaba ta kashin kai ba ne, illa don kare Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma dimokuraɗiyyar ƙasar.
Ya ce, “Ina alfahari da cewa na yi adawa da yunkurin wa’adi na uku. Ina alfahari da cewa na tsaya kan Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya. Ba ni da nadamar hana duk wani yunƙuri na murƙushe dimokuraɗiyya saboda wata manufa ta kashin kai.”
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa idan har Obasanjo na ci gaba da sukar sa saboda ya ƙi goyon bayan tsawaita wa’adin mulki ba bisa doka ba, to yana ɗaukar hakan a matsayin abin girmamawa.
Atiku ya kuma tuna irin gudunmawar da ya ce ya bayar wajen dawowar Obasanjo kan mulki a shekarar 1999, inda ya bayyana cewa ya tsaya masa a lokacin da yake fuskantar ƙalubale, ya taimaka wa iyalansa, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa ƙawancen siyasa da ya kai ga nasarar Obasanjo a zaɓe.
Ya ce duk da irin wannan gudunmawa, bai kamata a rika sauya tarihi ko rage rawar da ya taka ba.
Atiku ya kuma yi kira da a mayar da hankali kan manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta, kamar taɓarɓarewar tattalin arziki, matsalar tsaro da rashin aikin yi, maimakon ci gaba da tayar da tsoffin rikice-rikicen siyasa.
Martanin Atiku ya biyo bayan kalaman da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi a wani taro a Legas, inda ya bayyana cewa zaɓar Atiku a matsayin mataimakinsa a zaɓen shekarar 1999 shi ne mafi girman kuskuren da ya taɓa yi a rayuwarsa ta siyasa.
Add A Comment