Tawagar Najeriya ta ci gaba da nuna bajinta a Gasar Commonwealth ta 2026 da ake gudanarwa a Glasgow, inda ta kafa sabon tarihin gasar a tseren Mixed 4x400m Relay, tare da samun gurbi a wasu wasannin ƙarshe.
Ƴan wasan Najeriya Edidiong Udo, Esther Joseph, Samuel Ogazi da Patience Okon-George sun lashe zagayen share fage da lokaci na minti 3:14.58, wanda ya zama sabon tarihin gasar Commonwealth a wannan sabon nau’in tsere.
Najeriya ta doke Australia, wadda ta zo ta biyu da lokaci na minti 3:15.21, lamarin da ya tabbatar da cewa tawagar Najeriya ce ta fi sauri zuwa wasan ƙarshe, kuma tana cikin manyan masu neman lambar zinare.
A bangaren tsalle mai nisa, Ruth Usoro ta samu tikitin shiga wasan ƙarshe bayan ta yi tsalle mai nisan mita 6.77, wanda ya zarce ƙa’idar cancanta ta mita 6.70.
Haka kuma, Jami Schlueter na ci gaba da fafatawa a gasar men’s decathlon, inda yake matsayi na huɗu bayan kammala wasanni shida da maki 5,099. Ana sa ran zai kammala sauran wasanninsa da jifa da māshi da kuma tseren mita 1,500, inda yake da damar shiga cikin masu samun lambobin yabo.
A ci gaba da gasar, Ezekiel Nathaniel zai fafata a wasan ƙarshe na tseren mita 400 da shinge, yayin da Chinecherem Nnamdi zai shiga wasan ƙarshe na jifar māshi.
Haka kuma, fitaccen ɗan tsere Udodi Onwuzurike zai fafata a wasan ƙarshe na mita 200, inda yake fatan ƙara wa Najeriya yawan lambobin yabo.
Da wannan sabon tarihin da aka kafa da kuma yawan ƴan wasan da suka kai zagayen ƙarshe, Najeriya na da kyakkyawan fata na ƙara yawan lambobin yabonta a Gasar Commonwealth ta Glasgow 2026.
