Mai Martaba Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan Hijira.
Sarkin ya bayyana cewa Hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina ta kafa tubalin adalci, zaman lafiya, ‘yan uwantaka da gina al’umma, wadanda har yanzu duniya ke matukar bukata domin samun zaman lafiya da ci gaba.
A cikin sakon taya murnar da kakakinsa, Abdulazeez Arowona, ya fitar, Sarkin ya ce Hijira na tuna wa Musulmi muhimmancin hakuri, sadaukarwa da kuma dogaro ga Allah a dukkan al’amuran rayuwa.
Ya ce darasin Hijira shi ne cewa wahalhalu ba sa dawwama, don haka ya bukaci Musulmi su sabunta biyayyarsu ga Allah, su rungumi zaman lafiya tare da ci gaba da yi wa al’umma hidima.
Sulu-Gambari ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da sabuwar shekarar wajen yin addu’o’in zaman lafiya, hadin kai da bunkasar tattalin arziki a kasa baki daya.
Haka zalika, ya gargadi shugabannin addini da na siyasa da su guji kalaman da ka iya haddasa rikici ko rarrabuwar kawuna, tare da mayar da hankali wajen yada sakonnin da za su karfafa hadin kan kasa.
Sarkin ya yabawa Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai.
Ya kuma bukaci matasa da su yi koyi da jarumtaka, ladabi da biyayyar Musulman farko ta hanyar guje wa shaye-shayen miyagun kwayoyi, tashin hankali da sauran munanan dabi’u.
A wani bangare na sakonsa, Sarkin ya yi addu’ar Allah ya jikanta da gafara ga marigayi Farfesa Yusuf Lanre Badmos, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin tunawa da Hijira da yada darussan Musulunci a Jihar Kwara.
Daga karshe, ya yi addu’ar Allah Ya sanya sabuwar shekarar ta zamo sanadin alheri, lafiya, albarka da ci gaba ga Musulmi da daukacin al’ummar Najeriya.
