Kungiyar Kwara United ta sanar da cewa ranar Lahadi, 5 ga Yuli, 2026, ita ce ranar da dukkan ‘yan wasanta za su koma sansani domin fara shirye-shiryen kakar gasar Najeriya ta NPFL ta 2026/27.
Sanarwar da Shugaban kungiyar, Kumbi Titiloye, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa atisayen kafin fara kakar wasa zai fara ne daga ranar Litinin, 6 ga Yuli.
Kungiyar ta ce dukkan ‘yan wasan da aka ci gaba da rike su, tare da sabbin ‘yan wasan da masu horarwa suka zaba, ana sa ran za su isa sansani a ranar da aka tsara domin fara shirye-shiryen sabuwar kakar wasa.
Titiloye ya jaddada cewa wajibi ne kowane dan wasa ya halarta a kan lokaci, yana mai cewa mahukuntan kungiyar sun kuduri aniyar samar wa masu horarwa kyakkyawan yanayi domin gina kungiya mai karfi da za ta yi gogayya a kakar wasa mai zuwa.
Ya ce manufar kungiyar ita ce bai wa masu horarwa dukkan goyon bayan da suke bukata domin shirya kungiyar yadda ya kamata kafin fara kakar wasa.
Matakin fara atisayen tun da wuri ya biyo bayan kakar wasa ta 2025/26 mai cike da kalubale, inda Kwara United ta tsallake faduwa daga gasar NPFL ne a ranar karshe ta kakar.
Ana sa ran ‘yan wasan za su fara gwaje-gwajen lafiyar jiki da atisayen dabarun wasa a farkon shirin, yayin da masu horarwa ke kokarin inganta karfin kungiyar domin taka rawar gani a kakar 2026/27.
