Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kafa tsarin gudanar da Gwajin Kwarewar Dalibai na Kasa (National Learning Assessment) duk bayan shekaru uku, domin auna ingancin ilimi da kuma rage matsalar rashin kwarewar karatu da lissafi a tsakanin dalibai.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a bayan ya kai ziyara domin duba yadda ake gudanar da gwajin na shekarar 2026 a wasu makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke Kuje a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewarsa, gwajin ya shafi daliban aji uku da biyar na firamare, aji biyu na karamar sakandare (JSS2) da kuma aji biyu na babbar sakandare (SSS2), domin tantance kwarewarsu a fannin karatu, lissafi da fahimta.
Alausa ya ce daga shekarar 2029, Hukumar Ilimin Bai Daya ta Kasa (UBEC) za ta rika ware kudade a kasafin kudinta domin gudanar da wannan gwaji duk bayan shekaru uku.
Ya bayyana cewa gwajin na da matukar muhimmanci domin gano irin ilimin da ake bai wa yara da kuma tantance ko suna samun ilimin da ya dace.
Ministan ya ce rahotannin da suka gabata sun nuna cewa miliyoyin yara a Najeriya ba sa iya karanta rubutun da ya dace da shekarunsu idan sun kai shekara 10, yana mai cewa sabbin sauye-sauyen da gwamnati ke yi a bangaren ilimi za su taimaka wajen inganta sakamakon koyo.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta hade tsarin gwaje-gwaje daban-daban zuwa tsarin kasa guda domin tabbatar da daidaito da kuma saukaka kwatanta sakamakon koyo a tsawon lokaci.
Alausa ya ce wannan shiri na daga cikin manufofin sabunta bangaren ilimi na Najeriya, kuma ya yi daidai da kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta ilimi domin bunkasa ci gaban kasa.
Game da makarantu masu zaman kansu, ministan ya yaba da gudunmawar da suke bayarwa wajen kara yawan yaran da ke samun ilimi, amma ya jaddada bukatar kara tsaurara sa ido domin tabbatar da cewa suna bin ka’idojin da gwamnati ta gindaya.
A nasa bangaren, Sakataren Ilimi na Babban Birnin Tarayya (FCT), Dakta Danlami Hayyo, ya ce gwamnatin FCT ta gyara sama da makarantu 120 na gwamnati karkashin jagorancin Ministan FCT, Nyesom Wike.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin FCT za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya wajen aiwatar da shawarwarin da za su fito daga sakamakon wannan gwaji domin kara inganta ilimi a Najeriya.
