Fitacciyar ‘yar wasan kwallon Tennis ta Amurka, Coco Gauff, ta bayyana cewa wani lokaci ta yi kuka bayan yadda jami’an masu gudanar da gwajin hana amfani da kwayoyin kara kuzari (anti-doping) suka yi mu’amala da ita.
Gauff ta bayyana hakan ne bayan ta doke Tamara Korpatsch a zagayen farko na gasar, inda ta yi bayani kan yadda tsarin gwajin na International Tennis Integrity Agency (ITIA) ke gudana.
Ta ce ‘yan wasa dole ne su bayyana sa’a guda a kowace rana da za su kasance a wani wuri domin jami’an gwaji su same su, amma ana iya yi musu gwaji a wasu lokuta idan an same su.
‘Yar wasan mai shekaru 22 ta ce wasu jami’an gwajin kan yi magana cikin tsauri har hakan ke sa ‘yan wasa su ji kamar sun aikata wani laifi.
Ta tuna wani lokaci da wata jami’ar gwajin ta kira ta a lokacin da ba ya cikin lokacin da ta ware domin gwajin.
“Yadda ta yi magana da ni a waya ya sa na yi kuka bayan na gama kiran,” in ji Gauff.
Daga baya, Gauff ta ce ta gano cewa tana cikin hakkinta na kin amsa wannan bukata domin ba ta cikin lokacin da ta ware domin gwajin.
Duk da wannan lamari, Gauff ta ci gaba da mayar da hankali kan gasar, inda bayan nasarar da ta samu a zagayen farko, ta sake doke Solana Sierra a wasa mai zafi da ya kai zuwa kafa uku a ranar 1 ga Yuli.
