Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage zuwa 22 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da sauraron karar da fitaccen jarumin Nollywood, Emeka Ike, ya shigar kan neman diyya ta Naira biliyan 10 a kan zargin keta masa hakkin sirri.
Jarumin ya shigar da karar ne a kan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma Lere Olayinka, mai taimaka wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan harkokin yada labarai.
Yayin zaman kotun, lauyan Emeka Ike, L.T. Adeh, ya shaida wa kotu cewa daya daga cikin wadanda ake kara ya gabatar da amsarsa, amma INEC ba ta halarci zaman ba, duk da cewa an aika mata da takardar sanarwa.
Mai shari’a, Justice S.O. Ibrahim, ya ce ya dage shari’ar ne domin bai wa INEC damar bayyana a gaban kotu, tare da umartar a sake mika mata dukkan takardun karar kafin ranar zama ta gaba.
Shari’ar ta samo asali ne bayan wasu hotunan bayanan rajistar zaben Emeka Ike da suka nuna an canja rajistarsa daga Jihar Imo zuwa Babban Birnin Tarayya (FCT) suka bayyana a shafukan sada zumunta.
Emeka Ike na zargin cewa Lere Olayinka ya wallafa bayanan ne ba tare da izininsa ba, bayan an samu damar shiga wani tsarin bayanan sirri na INEC.
Jarumin na neman kotu ta ba shi diyya ta Naira biliyan 10, tare da umartar a goge sakon da aka wallafa a kafafen sada zumunta da kuma neman afuwa a bainar jama’a.
Sai dai lauyan Lere Olayinka, Akpama Ekwe, ya ce babu wani laifi da wanda yake karewa ya aikata, yana mai cewa bayanan da aka wallafa ba su kunshi cikakkun bayanan sirrin Emeka Ike ba.
A nata bangaren, INEC ta bayyana cewa lamarin bai faru sakamakon kutse a tsarin bayananta ba, sai dai saboda amfani da wasu sahihan bayanan shiga tsarin ta hanyar da ba ta dace ba.
