Reshen Jam’iyyar Labour Party (LP) na Jihar Abia ya kaddamar da gasar rubutun makala ga daliban makarantun sakandare da manyan makarantu, inda ya ware jimillar Naira miliyan 2.8 a matsayin kyaututtuka.
Sakataren jam’iyyar a jihar, Chuks Akamadu, ya bayyana hakan yayin kaddamar da gasar a hedikwatar jam’iyyar da ke Umuahia ranar Alhamis.
Ya ce gasar na da nufin karfafa matasa su shiga harkokin mulki da siyasa, tare da ba su damar bayar da shawarwari da za su taimaka wajen ci gaban Jihar Abia.
A cewarsa, taken gasar shi ne:
“The New Abia and Need for Consolidation” (Sabuwar Abia da Bukatar Dorewar Ci Gaba).
Akamadu ya ce an raba gasar gida biyu:
Ga daliban sakandare:
Wanda ya zo na farko zai samu Naira 500,000.
Na biyu zai samu Naira 300,000.
Na uku zai samu Naira 250,000.
Ga daliban manyan makarantu:
Wanda ya zo na farko zai samu Naira miliyan 1.
Na biyu zai samu Naira 500,000.
Na uku zai samu Naira 250,000.
Ya kara da cewa za a kuma ba wasu fitattun mahalarta kyaututtukan karfafa gwiwa, yayin da makarantun wadanda suka yi nasara za su samu karramawa ta musamman.
A cewarsa, rubutun bai kamata ya wuce kalmomi 1,500 ba, kuma dole ne a aika da shi ta adireshin imel na jam’iyyar kafin 17 ga Yuli, 2026, yayin da za a gudanar da bikin bayar da kyaututtuka ranar 3 ga Agusta, 2026.
Akamadu ya yabawa Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, bisa abin da ya bayyana a matsayin nasarorin gwamnatinsa cikin shekaru uku da suka gabata, yana mai cewa hakan ne ya zaburar da jam’iyyar ta shirya wannan gasa domin bai wa matasa damar ba da gudummawa ga ci gaban jihar.
