Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Deyemi Okanlawon, ya bayyana cewa ya taba barin harkar fim gaba daya a shekarar 2019 saboda rashin gamsuwa da karancin albashi da kuma irin rawar da ake ba shi.
Jarumin ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin CreativiTea Podcast, inda ya ce ya yanke shawarar komawa aikin kamfani bayan ya ga irin sadaukarwar da ya yi domin harkar fim ba ta ba shi gamsuwa.
A cewarsa, albashin da ake biya da kuma irin ayyukan da yake samu ba su dace da irin burinsa ba, lamarin da ya sa ya daina fitowa a fina-finai na wani lokaci.
Bayan barin Nollywood, Deyemi ya koma aiki a kamfanin Silverbird Film Distribution, inda ya fara a matsayin shugaban sashen kasuwanci (Head of Marketing), sannan daga baya ya jagoranci sashen rarraba fina-finan Nollywood. A lokacin annobar COVID-19 kuma, ya rike mukamin mukaddashin Babban Daraktan kamfanin.
Jarumin ya ce abin mamaki shi ne bayan ya fice daga Nollywood ne manyan masu shirya fina-finai suka fara neman ya dawo aiki.
Ya ambaci fitattun masu shirya fina-finai kamar Mo Abudu, Kemi Adetiba, Jade Osiberu, Funke Akindele da Kunle Afolayan a matsayin wadanda suka tuntube shi domin yin aiki tare.
Deyemi ya ce daga bisani ya amince ya koma harkar fim a shekarar 2021, kuma dawowarsa ta zo da sabbin damammaki.
Ya bayyana cewa fitowarsa a fim din “Omo Ghetto: The Saga” na Funke Akindele ta taimaka matuka wajen farfado da aikinsa, inda daga nan ya ci gaba da samun manyan guraben fitowa a fina-finan Nollywood.
Jarumin ya kara da cewa tafiyarsa a harkar fim ta fara ne tun a shekarar 2010, lokacin da ya samu damar fitowa a fina-finansa na farko.
