An samu zaman cike da cece-kuce a Majalisar Wakilai a ranar Laraba bayan wasu ‘yan majalisa sun yi sabani kan kudirin da ke neman a gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi bayani kan zargin rashin sakin kudaden ayyukan mazabu.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Aba ta Arewa da Kudu a Jihar Abia, Alex Mascot Ikwechegh, ne ya gabatar da kudirin, inda ya bukaci shugaban kasa ya bayyana dalilan jinkirin sakin kudaden ayyukan mazabu a fadin kasar.
An mara wa kudirin baya, yayin da wani dan majalisa ya nemi a dakatar da zaman majalisar na tsawon mako guda har sai an warware matsalar.
Sai dai dan majalisar APC daga Jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ya yi fatali da bukatar, yana mai cewa aiwatar da ayyukan mazabu da sakin kudaden su na karkashin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ne, ba shugaban kasa kai tsaye ba.
Hakan ya haddasa cacar baki da hayaniya tsakanin ‘yan majalisar, lamarin da ya sa Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya shiga tsakani domin kwantar da tarzomar.
Daga bisani, Kakakin Majalisar ya yanke hukuncin cewa bukatar gayyatar Shugaba Tinubu ba ta dace ba, saboda ba ta cikin ainihin kudirin da aka gabatar tun farko. Ya kuma umarci a ci gaba da bin hanyoyin da dokokin majalisa suka tanada wajen yanke hukunci kan sauran batutuwan da ke cikin kudirin.
