Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta yabawa Jakadan Najeriya a Côte d’Ivoire, Ambasada Nwabiola C. Ezenwa, da ma’aikatan ofishin jakadancin bisa ƙoƙarin diflomasiyya da suka yi wanda ya kai ga sakin ‘yan Najeriya da aka tsare a ƙasar.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce jakadan da ma’aikatansa sun nuna ƙwazo da jajircewa wajen tabbatar da an warware lamarin cikin nasara.
Sanarwar ta ce ofishin jakadancin ya ci gaba da kai ziyara ga ‘yan Najeriyar da ake tsare da su, ya kula da jin daɗinsu yayin da suke tsare, tare da yin tattaunawa akai-akai da Ma’aikatar Harkokin Wajen Côte d’Ivoire, Ma’aikatar Shari’a da sauran hukumomin ƙasar domin tabbatar da sakinsu.
Ma’aikatar ta kuma gode wa Gwamnatin Côte d’Ivoire bisa haɗin kai da ta bayar, tana mai cewa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar.
Ta sake jaddada cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta ci gaba da kare haƙƙoƙi, mutunci da jin daɗin ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje ta hanyar ofisoshin jakadancinta.
Sanarwar ta ƙara da cewa kula da walwala da kare ‘yan Najeriya a ƙetare na daga cikin manyan manufofin harkokin wajen ƙasar.
A ƙarshe, ma’aikatar ta shawarci ‘yan Najeriya da ke rayuwa ko tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje da su rika mutunta dokokin ƙasashen da suke ciki, sannan su kasance suna hulɗa da ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa idan bukatar hakan ta taso.
