Hukumar Kwallon Kafa ta Masar ta bukaci FIFA ta gudanar da bincike tare da cire alkalan da suka jagoranci wasan da Argentina ta doke Masar da ci 3-2 a zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya ta 2026.
A cikin wata sanarwa, shugaban hukumar kwallon kafar Masar, Hany Aburida, ya ce alkalin wasa dan Faransa, François Letexier, da tawagarsa sun tafka manyan kura-kurai da suka jawo wa Masar rashin nasara da kuma ficewa daga gasar.
Masar ta yi zargin cewa an soke kwallon da Mostafa Ziko ya ci bayan duba ta hanyar VAR, duk da cewa tana ganin hukuncin bai dace ba. Haka kuma ta ce ya kamata a ba ta bugun fenariti kafin Argentina ta ci kwallon da ta tabbatar da nasararta, amma alkalan sun yi watsi da lamarin.
Hukumar ta kuma bukaci a binciki dukkan alkalan VAR, tana mai cewa an nuna son kai ta hanyar kin duba wasu bidiyoyi da za su iya amfani wa tawagar Masar.
Kocin Masar, Hossam Hassan, shi ma ya bayyana cewa an zalunci kasarsa a wasan, yana mai cewa ba a gudanar da wasan cikin adalci ba.
Ya kara da cewa akwai yiwuwar an fifita Argentina domin ci gaba da kasancewa a gasar, yana mai ikirarin cewa zakarun duniya sun samu goyon baya a matakai daban-daban. Duk da haka, FIFA ba ta fitar da wata sanarwa kan korafe-korafen Masar ba.
