Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya kai ziyarar ban girma ga dan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben gwamna da aka kammala kwanan nan, Ambasada Dare Bejide, a gidansa da ke Ado-Ekiti.
Ziyarar da gwamnan ya kai a ranar Litinin na daga cikin shirinsa na tuntubar dukkan ‘yan takarar da suka fafata a zaben domin neman hadin kansu da shawarwarinsu wajen gudanar da mulkin jihar.
Oyebanji ya samu rakiyar mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Cif Jide Awe, yayin ziyarar, inda Ambasada Bejide ya tarbe su.
Rahotanni sun ce bangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin bunkasa ci gaban Jihar Ekiti da kuma yadda za a hada kai domin anfani al’umma.
Bayan sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 20 ga Yuni, Gwamna Oyebanji ya tuntubi dan takarar PDP, Dr. Wole Oluyede, da na ADC, Ambasada Dare Bejide, ta wayar tarho, inda ya yi alkawarin kai musu ziyarar kai tsaye.
Tun kafin wannan ziyara, gwamnan ya kai irin wannan ziyara gidan Dr. Wole Oluyede tare da wasu shugabannin jam’iyyar.
Gwamnatin Oyebanji ta bayyana cewa manufar irin wadannan ziyare-ziyare ita ce karfafa hadin kai, zaman lafiya, fahimtar juna da mutunta ra’ayoyin kowa, domin samar da ci gaba mai dorewa a Jihar Ekiti.
