Fitaccen tauraron kwallon kwando na duniya, LeBron James, ya taya dan wasan gaban tawagar Amurka, Folarin Balogun, murnar zura kwallo bayan ya yi amfani da shahararren salon murnar kwallonsa mai suna “Silencer” a wasan Kofin Duniya.
Balogun ya zura kwallo a wasan da Amurka ta doke Bosnia da Herzegovina da ci 2-0, inda ya yi bikin “Silencer” bayan kowace kwallo. Sai dai alkalin wasa ya soke kwallon farko saboda satar gida (offside).
LeBron James ya wallafa sako a shafinsa na X, yana cewa:
“Silencer ya isa Kofin Duniya! Kyakkyawar kwallo, matashin sarki.”
Sakon nasa ya samu kusan miliyan hudu na masu kallo cikin kankanin lokaci.
Shahararren bikin “Silencer” na LeBron ya hada da daga gwiwoyi, tura tafukan hannu kasa da kuma buga kirji, alamar cewa ya yi shiru da masu adawa ko masu sukar sa.
Balogun mai shekaru 24, wanda aka haifa a New York, ya taso a London kuma yanzu yana taka leda a Faransa, sanannen masoyin wasan kwallon kwando ne.
Rahotanni sun ce lokacin da Amurka ke kokarin shawo kansa ya wakilci kasar maimakon Ingila ko Najeriya, an kai shi Florida tare da ba shi damar kallon wasan NBA daga kusa da filin wasa.
Balogun ya zuwa yanzu ya zura kwallaye uku a gasar Kofin Duniya ta 2026, inda Amurka ta kai zagayen ‘yan wasa 16. Sai dai ba zai buga wasan da za su kara da Belgium ba bayan da aka ba shi jan kati a rabin na biyu na wasan da Bosnia da Herzegovina.
A gefe guda kuma, LeBron James mai shekaru 41 ya sanar da cewa zai bar kungiyar Los Angeles Lakers, amma zai ci gaba da taka leda a kakarsa ta 24 a NBA tare da wata sabuwar kungiyar.
