Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta gurfanar da wani babban likitan cutar daji a Asibitin Kasa da ke Abuja, Dr. Bello Abubakar, bisa zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi da aka ce an yi amfani da shi wajen neman beli ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A cewar takardun ƙarar da aka shigar, ICPC ta tuhumi likitan da laifuffuka guda huɗu, ciki har da bayar da bayanan ƙarya, amfani da mukaminsa ba daidai ba, haɗa baki wajen ƙirƙirar bayanan bogi, da kuma amfani da takardar da ba ta da sahalewar Asibitin Kasa.
Hukumar ta ce rahoton lafiyar mai taken “Medical Report and Expert Opinion for Urgent Medical Intervention”, mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Yuni, 2026, an yi amfani da shi ne domin tallafawa buƙatar neman belin El-Rufai a wata shari’a da ke gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.
Binciken ICPC ya nuna cewa an gabatar da rahoton ga Kwamishinan Rantsuwa kafin a shigar da shi a kotu, duk da zargin cewa bayanan da ke cikinsa ba gaskiya ba ne.
Haka kuma, Asibitin Kasa ya bayyana wa ICPC cewa bai ba da izinin fitar da rahoton ba, kuma binciken bayanan marasa lafiya bai gano wata shaida da ke nuna El-Rufai ya kasance majiyyaci a lokacin da aka rubuta rahoton ba.
Sai dai Dr. Bello Abubakar ya shaida wa masu bincike cewa El-Rufai ya kasance majiyyacin Asibitin Kasa tun shekara ta 2005, yana mai cewa ya duba lafiyarsa sau da dama, ko da yake wasu daga cikin ziyarce-ziyarcen ba a rubuta su a hukumance ba.
ICPC ta bayyana cewa za ta gabatar da manyan shaidu a shari’ar, ciki har da Babban Daraktan Asibitin Kasa, Dr. Raji Mahmud, jami’in binciken hukumar da sauran takardun da suka shafi binciken.
A halin yanzu, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na fuskantar wasu shari’o’in cin hanci da rashawa da ICPC ta shigar a kansa, ciki har da zargin almundahana a kwangilar tsarin sa ido na CCTV da ta kai kimanin Naira biliyan 8.68, zarge-zargen da ya musanta tare da bayyana cewa ba shi da laifi.
