Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba a dakatar da ayyukan fitar da fasfo a faɗin ƙasar ba, duk da sauya wasu rassan cibiyoyin sarrafa fasfo zuwa Central Personalization Centre.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, hukumar ta bayyana cewa sauyin wani mataki ne na inganta tsarin gudanar da aikin fitar da fasfo da kuma ƙara matakan tsaro, ba wai dakatar da ayyukan ba.
Hukumar ta ce masu neman fasfo za su ci gaba da zuwa cibiyoyin da aka ware musu domin yin rajistar bayanan halitta (biometric capture) ba tare da wata matsala ba.
Ta bayyana cewa sabon tsarin samar da fasfo daga cibiyar guda zai taimaka wajen daidaita aikin da ƙa’idojin tsaro na duniya, rage jinkiri wajen sarrafa buƙatu da kuma kare ingancin fasfon Najeriya.
NIS ta kuma tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin ɗaukar bayanan masu neman fasfo na ci gaba da aiki yadda ya kamata, yayin da ake ci gaba da buga littattafan fasfo da rabawa ofisoshin hukumar cikin wa’adin da aka saba.
Hukumar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, tana mai jaddada cewa babu wani cikas ga ayyukan neman ko karɓar fasfo a faɗin Najeriya.
