Jami’ar Legas (UNILAG) ta taya ɗaya daga cikin ɗalibanta, Peter A. Fagbola, murnar lashe babbar gasar Huawei Global ICT Competition da aka gudanar a birnin Shenzhen na ƙasar China.
Fagbola, ɗalibi ne a Sashen Systems Engineering na Tsangayar Injiniya kuma mamba na ABS-CITS Huawei Academy. Ya kasance cikin Team Nigeria Cloud, wadda ta lashe matsayi na farko a gasar tare da samun kyautar kuɗi ta Naira miliyan 3.5.
Gasar Huawei Global ICT na ɗaya daga cikin manyan gasar fasaha mafi daraja a duniya, inda dubban ɗaliban jami’o’i daga ƙasashe daban-daban ke fafatawa.
A cewar sanarwar da jami’ar ta fitar, tafiyar Fagbola zuwa matakin duniya ta fara ne bayan ya zama zakara a rukunin Cloud and AI Track a gasar matakin Najeriya yayin da yake wakiltar UNILAG.
Daga bisani, shi da takwarorinsa sun lashe gasar yankin Kudancin Afirka, wanda ya ba Najeriya damar wakilci a wasan ƙarshe na duniya da aka gudanar a Shenzhen.
A gasar ta duniya, Team Nigeria Cloud ta doke ƙungiyoyi daga ƙasashe daban-daban tare da lashe kambun zakara da kyautar Naira miliyan 3.5.
UNILAG ta bayyana cewa wannan nasara tana nuna ƙwazo da jajircewar Fagbola, tare da ingancin horo da kulawar da jami’ar ke bai wa ɗalibanta.
Jami’ar ta ƙara da cewa bayan wannan nasara, an gayyaci Fagbola zuwa Huawei Education Summit da aka gudanar a Abuja, inda aka karrama shi tare da sauran waɗanda suka yi fice.
Shugabar Jami’ar UNILAG, Farfesa Folasade Ogunsola, ta taya Fagbola murna a madadin jami’ar baki ɗaya, tana mai fatan zai ci gaba da samun manyan nasarori a nan gaba.
Jami’ar ta ce wannan gagarumar nasara ta zama abin koyi ga sauran ɗalibai domin su himmatu wajen neman ilimi da fafatawa a gasa ta ƙasa da ƙasa.
