Jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Kenneth Okonkwo, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan kare Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), yana mai cewa har yanzu hukumar ba ta tabbatar wa ’yan Najeriya da cikakken adalci da rashin son kai ba.
Tinubu ya bayyana a wani taro da shugabannin Ƙungiyar Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN) a Abuja cewa INEC hukuma ce mai cin gashin kanta, tare da cewa masu shakkar sahihancinta suna “tsoron inuwarsu.”
Sai dai da yake magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels TV, Okonkwo ya ce bai kamata Shugaban Ƙasa ya zama mai kare INEC ba, yana mai cewa hukumar ce ya kamata ta fito ta yi bayani kan zarge-zargen da ake yi mata.
Ya ce, “Abin takaici ne shugaban ƙasa ya zama babban mai magana da yawun INEC. Wannan alama ce mai nuna damuwa ga dimokuraɗiyyar ƙasa.”
Okonkwo ya ce har yanzu akwai tambayoyi da dama da INEC ba ta amsa ba, musamman game da matsalolin da suka taso a zaɓen shekarar 2023, ciki har da matsalar fasaha da aka samu wajen gudanar da zaɓen.
Ya kuma tunatar da cewa Tinubu da jam’iyyarsa sun kasance masu sukar INEC a shekarar 2015, amma yanzu suna bayyana cewa hukumar tana gudanar da aikinta cikin adalci.
Bugu da ƙari, Okonkwo ya soki gwamnatin Tinubu kan yadda take tafiyar da harkokin tsaro da mulki, yana mai cewa hakan na iya rage masa damar sake samun wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Ya kuma yi kira ga Tinubu da ya yi murabus maimakon neman sake tsayawa takara.
Dangane da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya soke umarnin da ya bukaci INEC ta cire rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu, Okonkwo ya ce jam’iyyarsa ta yi nasarar dakile ƙoƙarin da ake yi na hana ta ci gaba da wanzuwa ta hanyar shari’a.
A ƙarshe, ya zargi jam’iyyar APC da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa da kuma tauye fafatawar siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
