Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agusta ba kawai fafatawar neman nasara ba ce, illa wata dama ce ta isar da saƙo ga Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan muhimmancin mutunta zaɓin al’umma.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, Adeleke ya zargi Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Gboyega Oyetola, da ɗan takarar gwamnan APC, Bola Oyebamiji, da amfani da tasirinsu a gwamnatin tarayya domin hukunta al’ummar Osun saboda zaɓensa da suka yi a zaɓen shekarar 2022.
A cewarsa, nasara mai ƙarfi a zaɓen 15 ga Agusta za ta nuna wa APC cewa dole ne a mutunta ra’ayin masu kaɗa ƙuri’a, kuma babu wanda ya kamata ya hukunta jama’a saboda sun yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe.
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa matakan da Oyetola da Oyebamiji suka ɗauka sun shafi jin daɗin ma’aikatan gwamnati tare da barazana ga rayuwar ma’aikata, ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da sauran al’ummar jihar.
Ya ce al’ummar Osun suna da ‘yancin zaɓar shugabannin da suke so ba tare da fuskantar wani nau’i na takura ko ramuwar gayya ba.
Kalaman Adeleke na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin gwamnatin jihar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) kan wasu batutuwa da suka shafi harkokin kuɗi na jihar
