Jazmyne Wike, ‘yar Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ta kammala karatun digirin lauya (LL.B.) tare da samun Upper Second-Class Honours daga Jami’ar Southampton da ke Birtaniya.
Jazmyne ta samu wannan nasara ne bayan ta kammala karatunta cikin nasara a daya daga cikin fitattun jami’o’in kasar Birtaniya.
Nasarar tata ta jawo sakonnin taya murna daga iyalai, abokai da sauran masu fatan alheri, inda suka yabawa kokarinta da nasarar da ta samu a fannin ilimi
