Hukumar Hana Safarar Bil Adama ta Kasa (NAPTIP) ta bayyana cewa ta ceto mutane 156 da suka fada hannun masu safarar bil adama tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2026.
Babbar Daraktar Hukumar, Binta Bello, ta bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai gabanin Ranar Yaki da Safarar Bil Adama ta Duniya.
Ta ce masu safarar bil adama na amfani da tayin ayyukan yi na bogi a kasashen ketare domin yaudarar matasa ‘yan Najeriya masu ilimi, musamman da alkawuran aikin fasahar sadarwa, kasuwancin intanet da sauran ayyuka masu albashi mai tsoka.
A cewarta, da zarar wadanda aka yaudara sun isa wasu kasashen Kudu maso Gabashin Asiya, ana kwace musu fasfofinsu tare da tilasta musu gudanar da damfara ta intanet karkashin barazana da azabtarwa.
Bello ta kara da cewa sama da ‘yan Najeriya 300 da aka yi safararsu zuwa Ghana da Cote d’Ivoire an dawo da su gida a shekarar 2025, yayin da NAPTIP ta samu hukuncin kotu guda 47 kan masu laifin safarar bil adama tsakanin Janairu da Yuli 2026.
Hukumar ta kuma bukaci matasa su guji amincewa da tayin aikin yi daga hanyoyin da ba su da tabbaci, tare da kira ga iyaye da al’umma su kara wayar da kan matasa kan hadarin safarar bil adama.