Wata kotun tarayya a Amurka ta sanya 1 ga Yuni, 2027 a matsayin ranar fara shari’ar tsohon shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, da matarsa Cilia Flores, bayan an gurfanar da su kan zargin safarar miyagun kwayoyi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Maduro da matarsa sun shafe sama da watanni bakwai a gidan yari da ke Brooklyn tun bayan kama su a watan Janairun 2026, inda suka musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Alkalin kotun, Alvin Hellerstein, ya kuma sanya ranar 17 ga Nuwamba, 2026 domin sauraron bukatun lauyoyin bangarorin biyu, ciki har da kalubalantar yadda aka kama ma’auratan.
Masu gabatar da kara sun zargi Maduro da amfani da karfin gwamnati wajen kare masu safarar hodar iblis zuwa Amurka, zargin da shi da matarsa suka musanta.
A waje da kotun, wasu masu zanga-zanga sun bukaci a saki Maduro, yayin da wasu kuma suka bayyana shi da matarsa a matsayin masu mulkin kama-karya.
Har ila yau, Maduro na fuskantar wata kara ta farar hula a Amurka kan zargin hannu a kashe-kashen da ake zargin jami’an tsaro suka aikata a lokacin mulkinsa tsakanin shekarun 2013 zuwa 2026.
