Hukumar Kwastam ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta sanar da fitar da jerin sunayen ƙarshe na waɗanda suka yi nasarar samun aikin daukar ma’aikata na shekarar 2024/2025, inda mutane 3,852 suka samu guraben aiki bayan shafe watanni 20 ana gudanar da aikin tantancewa.
Babban Kwanturola Janar na Hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda suka yi nasara, mutum 1,275 sun samu gurbi a rukunin Superintendent Cadre, 367 a Inspectorate Cadre, yayin da 2,210 suka shiga Customs Assistant Cadre.
Adeniyi ya nemi afuwar dubban matasan Najeriya da iyalansu saboda jinkirin da aka samu wajen kammala aikin daukar ma’aikatan, yana mai cewa hukumar ta ɗauki lokaci ne domin tabbatar da an zaɓi waɗanda suka cancanta.
Ya bayyana cewa hukumar ta karɓi jimillar 573,680 na buƙatun neman aiki domin guraben 3,852 kacal, inda aka tantance kowane mai neman aiki ta hanyoyi daban-daban, ciki har da gwajin kwamfuta da kuma tabbatar da sahihancin bayanai ta hanyar bayanan katin shaidar ɗan ƙasa (NIN).
A cewarsa, daga cikin masu neman aikin, mutum ɗaya ne kacal ya samu aiki cikin kusan mutane 148, lamarin da ya nuna irin tsananin gasa da aka yi.
Ya ce rukunin Inspectorate Cadre shi ne ya fi samun gasa, inda mutum ɗaya kawai ya samu aiki cikin masu nema 350, yayin da Superintendent Cadre ya kasance mutum ɗaya cikin 217, sannan Customs Assistant Cadre mutum ɗaya cikin 76.
Kwanturola Janar ɗin ya ƙara da cewa an gudanar da daukar aikin bisa tsarin Federal Character, inda kowace jiha daga cikin jihohi 36 ta samu gurabe 105, yayin da Babban Birnin Tarayya (FCT) ya samu gurabe 72.
Ya kuma bayyana cewa mata 839 ne suka yi nasara, wanda ya kai kashi 21.8% na adadin waɗanda aka ɗauka, yana mai cewa hukumar za ta ƙara ƙoƙarin jawo mata da dama su shiga aikin Kwastam a daukar ma’aikata na gaba.
Adeniyi ya shawarci waɗanda ba su yi nasara ba da kada su karaya, yana mai tabbatar musu cewa za a sake buɗe daukar ma’aikata nan gaba, tare da gargadin jama’a da su guji masu damfara da ke karɓar kuɗi da sunan samar da aiki a Hukumar Kwastam.
