Lauya kuma mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Hamza Dantani, ya yi kira ga hukumomin tsaro a Najeriya da su kafa tsarin biyan diyya ga mutanen da aka kama ko aka tsare ba bisa ka’ida ba, ko kuma suka samu illa sakamakon ayyukan jami’an tsaro, yana mai cewa su yi koyi da tsarin da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta fara aiwatarwa.
A cikin wata sanarwa mai taken “DSS Compensation Initiative Sets Standard for Security Agencies”, Dantani ya yaba wa Darakta Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, bisa ƙaddamar da tsarin biyan diyya ga waɗanda suka zama waɗanda aka zalunta sakamakon kuskuren jami’an tsaro.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi da zai ƙara tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.
A cewarsa, yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka yana da muhimmanci, amma dole ne a gudanar da shi cikin bin doka tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam.
Dantani ya ce hukumomin tsaro ba wai kawai suna da alhakin kare ƙasa ba, har ila yau suna da nauyin amincewa da kuskuren da aka tafka da kuma bai wa waɗanda aka zalunta hakkinsu.
Ya kawo misalan wasu da suka amfana da tsarin biyan diyya na DSS, ciki har da Nura Idris daga Kaduna, wanda aka ce ya samu Naira miliyan 3 bayan an kama shi bisa kuskuren zargin alaƙa da Boko Haram.
Haka kuma ya ambaci Chineze Ozoadibe, ‘yar kasuwa daga Abuja, wadda aka ce ta samu Naira miliyan 10 bayan an kama ta bisa zargin safarar haramtaccen mai da daga baya aka tabbatar ba ta da laifi.
Sauran da ya ambata sun haɗa da wani ɗan kasuwa daga Sokoto da aka ce ya samu Naira miliyan 20 tare da kulawar lafiya na tsawon rayuwa bayan an harbe shi bisa kuskure a wani samame, da kuma wasu mutane da aka kama bisa zargin garkuwa da mutane da ta’addanci amma daga baya aka wanke su tare da ba su diyya.
Dantani ya kuma bukaci hukumomi irin su ‘Yan Sandan Najeriya, Sojojin Najeriya, NSCDC, EFCC, NDLEA da sauran hukumomin tsaro su samar da irin wannan tsari na biyan diyya ga mutanen da aka kama ko aka cutar ba tare da sun aikata laifi ba.
Ya kuma ba da shawarar inganta tattara bayanan sirri, tabbatar da sahihancin bayanan mutane, amfani da binciken kimiyya, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma horas da jami’an tsaro kan mutunta haƙƙin ɗan Adam domin rage yawan kama mutane ba bisa ƙa’ida ba.
A ƙarshe, Dantani ya ce ainihin adalci ba wai hukunta masu laifi kaɗai ba ne, har da kare marasa laifi, amincewa da kuskure idan ya faru, da kuma ba waɗanda aka zalunta diyya da ta dace.
