Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi manyan kamfanonin mai da cin gajiyar rikicin yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran wajen samun riba mai yawa, tare da buƙatar su rage farashin mai ga masu amfani da kuma mayar da wani ɓangare na ribar da suka samu.
Da yake magana da manema labarai a Fadar White House, Trump ya ce kamfanonin mai kamar ExxonMobil da Chevron suna cin moriyar fargabar ƙarancin mai da rikicin ya haifar.
Ya ce, “Suna samun riba mai yawa saboda ƙarancin mai. Ban ji daɗin hakan ba.”
Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi daga kusan dala 70 kan ganga kafin barkewar rikicin zuwa kusan dala 126 kafin daga bisani ya sauka zuwa kusan dala 85.
Sakamakon hauhawar farashin, kamfanonin ExxonMobil da Chevron sun samu haɗaɗɗiyar riba da ta haura dala biliyan 26 cikin watanni uku da suka ƙare a watan Yuni.
Chevron ta bayyana ribar dala biliyan 12.2, yayin da ExxonMobil ta sanar da ribar dala biliyan 14.5, mafi girma tun bayan yaƙin Rasha da Ukraine a shekarar 2022.
Trump ya ce kamata ya yi kamfanonin su mayar da wani ɓangare na ribar ga jama’a ta hanyar rage farashin man fetur.
A nata martanin, shugabar kamfanin BP, Meg O’Neill, ta ce farashin man fetur yana dogara ne da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, ba wai kamfanoni kaɗai ke kayyade shi ba.
Kungiyoyin kare muhalli ma sun soki ribar da kamfanonin mai suka samu, suna masu cewa al’umma ce ke ɗaukar nauyin tsadar makamashi yayin da kamfanonin ke ci gaba da tara riba.
Trump ya sake jaddada cewa ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta binciki yiwuwar tsadar farashin mai ba bisa ƙa’ida ba, tare da gargadin masu sayar da mai su rage farashin cikin gaggawa.
A halin yanzu, bayanan kungiyar AAA sun nuna cewa matsakaicin farashin galan ɗaya na fetur a Amurka ya kai dala 4.11.
Masana harkokin tattalin arziki sun ce idan farashin mai ya ci gaba da tashi, gwamnatin Amurka na iya sake duba wasu manufofi da suka shafi fitar da ɗanyen mai da sauran kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje.
