Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani kan zarge-zargen da ke cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa maso Yamma, inda ta bayyana cewa gwamnati na gudanar da manyan ayyuka masu yawa a yankin musamman a bangarorin sufuri, lafiya da ababen more rayuwa.
An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja karkashin kungiyar Renewed Hope Ambassadors, wacce ke shirin fara rangadin nuna ayyukan gwamnati a jihohin Arewa maso Yamma.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da ayyuka na musamman, Tunde Rahman, ya ce ikirarin cewa Tinubu bai cika alkawuransa ga Arewa ba ba gaskiya ba ne.
Ya ce daga cikin manyan ayyukan da ake yi akwai layin dogo na zamani na dala biliyan biyu daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, wanda ya kai kusan kashi 60 cikin 100 na kammalawa.
Rahman ya bayyana cewa manufar rangadin ita ce nuna wa ‘yan Najeriya irin ayyukan da gwamnatin ta yi a cikin shekaru uku domin kawar da rade-radin rashin aiki.
Shi ma mai bai wa shugaban kasa shawara kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce gwamnati ta fahimci cewa akwai gibin bayanai da ya sa mutane da dama ba su san ayyukan da ake yi ba.
A cewarsa, dole ne gwamnati ta fito ta nuna ayyukanta domin jama’a su gani da ido.
Daraktan kula da harkokin layin dogo na ma’aikatar sufuri, Finbarr Zirra, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na zama cibiyar manyan ayyukan layin dogo na kasa baki daya.
Ya ce layin Kaduna zuwa Kano ya kusa kammaluwa, yayin da ake sa ran layin Kano zuwa Katsina zai kammala nan da karshen shekara.
Haka kuma ana aikin wani reshen layi daga Kano zuwa Dutse, wanda zai kara bunkasa harkokin kasuwanci da sufuri a yankin.
Zirra ya bayyana cewa idan aka kammala wadannan ayyuka, Kano za ta zama babbar cibiyar layin dogo mafi girma a Najeriya.
Ya kara da cewa ingantaccen layin dogo zai rage cunkoson manyan motoci a hanyoyi, rage lalacewar tituna da saukaka safarar kaya.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa akwai shirye-shiryen kara zuba jari a layukan dogo masu sauri daga Lagos zuwa Kano da kuma Lagos zuwa Port Harcourt.
