Wani ɗan ƙasar Spain, Carlos Barragan, ya yi tattaki zuwa Legas domin gano mutanen da suka damfari mahaifiyarsa ta hanyar soyayyar intanet.
Barragan ya ce tun farko shi ne ya ƙarfafa mahaifiyarsa, wadda ta rabu da mijinta, ta gwada neman abokin rayuwa ta yanar gizo domin ta samu wanda za ta riƙa tare da shi.
Sai dai ba da daɗewa ba, mahaifiyar tasa ta haɗu da wani mutum da ya gabatar da kansa da suna Brian, yana ikirarin cewa sojan Amurka ne da ke aiki a Syria.
A cewar Barragan, mutumin ya yi wa mahaifiyarsa kyau sosai har ta ɗauke shi a matsayin cikakken mutumin da ta dade tana nema.
“Mutumin yana da kyau sosai. Mahaifiyata tana magana a kansa kamar wani basarake ne da ya shigo rayuwarta,” Barragan ya bayyana.
Sai dai bayan watanni biyu kacal da fara soyayyar, Brian ya gaya wa mahaifiyar Barragan cewa yana son ya zo ya zauna da ita, tare da kawo wasu sandunan zinariya da ya ce ya samo ne daga wani sansanin ‘yan ta’adda.
Wannan batu ya sa Barragan fara zargin cewa akwai wani abu da ba daidai ba.
Ya fara bincike, inda daga ƙarshe ya gano cewa adireshin IP da ake amfani da shi wajen sadarwa da mahaifiyarsa yana Legas, Najeriya, ba Syria ba.
Wannan bincike ya tabbatar masa da cewa mutumin da mahaifiyarsa ta kamu da soyayya da shi ba shi ne wanda ya yi ikirarin kasancewa ba.
Lamarin ya girgiza mahaifiyarsa, amma kuma ya sa Barragan fara tunanin wata babbar matsala da ke bayan irin waɗannan damfarar — kaɗaici.
Ya tambayi kansa yadda mutum da ke dubban kilomita daga mahaifiyarsa zai iya yaudararta har ta yarda da shi.
Domin samun amsoshi, Barragan ya yi tafiya zuwa Legas, inda ya fara ganawa da wasu matasa da ke hannu a damfarar soyayya ta intanet, domin fahimtar yadda suke gudanar da ayyukansu.
Daga cikin mutanen da ya haɗu da su akwai wani matashi mai suna Biggy, mai shekaru 29, wanda har yanzu yake zaune da iyayensa.
Barragan ya bayyana Biggy a matsayin mutum mai basira, barkwanci da tausayi, amma duk da haka yana cikin masu amfani da intanet wajen farautar tsofaffi a Amurka ta hanyar damfarar soyayya.
Wannan ganawa ta sa Barragan shiga ruɗani, domin ya kasa haɗa halayen mutanen da ya gani a zahiri da kuma irin yaudarar da suke yi a yanar gizo.
“Na ci gaba da tambayar kaina, ta yaya mutum irin sa zai zama ɗan damfara da yake kwana yana magana da mutanen da ke fama da kaɗaici a intanet?” ya ce.
Barragan ya ce maimakon ya tarar da wasu manyan ƙungiyoyin masu aikata laifuka masu tsari irin wanda ya yi zato, ya gano cewa da dama daga cikin matasan da ya haɗu da su ba su da cikakken ilimi, kuma suna amfani da wayoyi da intanet ne kawai wajen yaudarar waɗanda suke nema.
Ya ce abin ya ba shi mamaki yadda irin wannan hanya mai sauƙi za ta iya haifar da babbar illa ga mutane.
A cewarsa, wasu daga cikin masu damfarar da ya gana da su sun bayyana masa cewa dabararsu ita ce ba mutanen da ke fama da kaɗaici kulawa, su gina amana da su, sannan su ƙarfafa alaƙar soyayya kafin daga bisani su nemi kuɗi.
Barragan ya kuma gana da wani yaro mai suna Azeez, mai shekaru 15, wanda yake zaune da mahaifiyarsa da ƙanwarsa jaririya a wani ƙaramin gida.
Ya ce Azeez ya yi amfani da dala 5 na farko da ya samu daga damfarar intanet wajen zuwa gidan cin abinci domin cin kaza, abin da ya bayyana a matsayin karon farko da ya shiga wurin da ke da na’urar sanyaya iska.
Duk da cewa Barragan bai manta da irin asarar da waɗanda aka damfara suka yi ba, ciki har da mutanen da suka rasa makudan kuɗaɗe, ganawarsa da matasan ta sa ya fara fahimtar wasu daga cikin yanayin rayuwar da ke kewaye da su.
Bayan ganawa da sama da mutane 50 da ake zargi da damfarar intanet, da kuma tattaunawa da wasu daga cikin waɗanda aka cutar, Barragan ya koma wajen mahaifiyarsa da wata sabuwar fahimta da ya ce ta wuce batun Najeriya.
A cewarsa, kaɗaici a wasu ƙasashen Yamma na ƙara samar da damar da masu damfarar intanet ke amfani da ita wajen yaudarar mutane.
Ya ce wasu daga cikin matasan da ya gana da su ba su ma kammala makarantar sakandare ba, amma sun iya samun kuɗi daga mutanen da ke wasu ƙasashe.
Wannan ƙwarewar Barragan ta zama tushen littafinsa mai suna “The Yahoo Boys”, inda yake bayani kan duniyar damfarar intanet a Najeriya, matasan da ke cikinta da kuma mutanen da ke faɗawa tarkon dangantakar soyayya ta yanar gizo.
Barragan ya kuma ce abin da ya koya daga wannan tafiya shi ne cewa masu amfani da kafafen sada zumunta wajen neman soyayya su riƙa yin taka-tsantsan.
A takaice, idan wani mutum a intanet ya bayyana kamar ya fi kowa kyau, kirki da cika dukkan abin da kuke nema, ya dace a fara bincike kafin a yarda da shi — domin wani lokaci, abin da ya yi kyau fiye da kima na iya ɓoye wata babbar damfara.
