Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta ƙara tsaurara ayyukan bincike da ceto bayan rahoton yin garkuwa da wasu mutane a kan titin Okene-Auchi.
Kakakin rundunar, ASP Salisu Afusat, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, inda ta ce an tura jami’an ’yan sanda da sojoji domin gudanar da bincike a cikin dazuzzukan da ake zargin masu garkuwar ke amfani da su a matsayin mafaka.
Ta ce nan take bayan faruwar lamarin, rundunar ta ƙaddamar da bincike na musamman a yankunan dazuzzuka da ke tsakanin Okene da Ajokuta, musamman dajin Ebiya da sauran wuraren da ke kewaye da shi.
Aikin ya haɗa da jami’an rundunar ’yan sanda daga Okene, Mobile Force, Anti-Kidnapping Unit da sauran sassan rundunar, tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Najeriya.
Haka kuma, rundunar ’yan sandan Edo ta shiga aikin, musamman sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran jami’an dabaru.
Rundunar ta ce an ƙara ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa a iyakar Kogi da Edo, domin toshe duk wata hanyar tserewa ga masu laifin tare da gudanar da sintiri da bincike a wuraren da ake zargin suna da alaƙa da lamarin.
A yayin binciken, jami’an tsaro sun gano tare da bincika wasu wuraren da ake zargin masu laifin ke fakewa.
Daga cikin abubuwan da aka gano akwai kayan abinci da kayan girki, hular sojoji irin ta daji da kuma katin shaidar ɗan ƙasa, da wasu abubuwa da ake zargin masu laifin suka bari.
An kuma lalata tare da ƙona wuraren da aka gano domin hana masu laifin sake amfani da su.
Sai dai rundunar ta ce ba a samu wani daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ba a zagayen binciken farko, amma jami’an tsaro na ci gaba da kutsawa cikin dazuzzukan da yankunan da ke kusa da su domin gano inda ake tsare da waɗanda aka sace.
Sanarwar ta ce a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, jami’an dabaru sun ci gaba da kutsawa zuwa wuraren da aka gano a yankunan Ajaokuta da Adoko.
Haka kuma, an yi amfani da jiragen sama marasa matuƙi (drones) na Rundunar Sojin Najeriya da ’Yan Sandan Edo domin ƙara sa ido da tattara bayanan sirri.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, CP Naziru Kankarofi, ya umurci jami’an da ke gudanar da aikin da su ci gaba da bincike da ceto har sai an samu nasarar kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa masu laifin ba su tsere wa hukunci ba.
