Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta umarci dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajjin 2027 da suka riga suka yi rajista da su miƙa ingantattun fasfofinsu na ƙasa da ƙasa kafin ko zuwa ranar 25 ga Agusta, 2026.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Darakta-Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Matawalle, a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi domin kammala rajista da tantance bayanan dukkan maniyyatan Hajjin 2027 cikin lokaci.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi rajista amma bai miƙa fasfo dinsa zuwa ranar da aka kayyade ba, na iya rasa damar samun kujerar Hajji.
A cewar Darakta-Janar ɗin, an sanya ranar ƙarshe ne saboda buƙatar kammala dukkan matakan rajista da tattara bayanan mahajjata cikin lokacin da ya dace, musamman ganin ana sa ran rufe tsarin rajistar Hajjin Saudiyya a ƙarshen watan Agusta.
Hukumar ta buƙaci dukkan maniyyatan Kano da har yanzu ba su miƙa fasfo ba da su gaggauta yin hakan kafin ranar 25 ga Agusta, 2026.
Ta kuma bayyana cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wata matsala ko sakamakon da zai biyo bayan rashin bin wannan wa’adin ba.
Add A Comment
