Ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a zaɓen gwamnan Osun ya janye daga takararsa tare da bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, gabanin zaɓen da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026.
Ɗan takarar ya bayyana cewa ya yanke shawarar ne bayan tuntubar shugaban jam’iyyarsu na jihar, sakataren jam’iyyar da sauran manyan jami’ai.
Ya ce bayan tuntuba da tattaunawa, sun cimma matsaya cewa ya kamata su haɗa kai, yana mai cewa dukkaninsu masu kishin ci gaba ne.
“Na daɗe ina bibiyar ‘yan takarar, kuma bayan tuntubar shugaban jam’iyyarmu na jihar, sakatare da sauran manyan jami’ai, mun cimma matsaya. A ƙarshe dai, dukkanmu masu kishin ci gaba ne.”
Ya ƙara da cewa suna fatan da yardar Allah za su taimaka wajen kai Oyebamiji ga nasara a jihar Osun.
Da yake mayar da martani kan wannan goyon baya, Oyebamiji ya yaba da matakin da ɗan takarar APGA ya ɗauka, tare da bayyana cewa yana shirin tuntuɓar sauran jam’iyyun siyasa domin neman goyon bayansu a zaɓen.
Oyebamiji ya ce haɗin kan jam’iyyun siyasa zai taimaka wajen kawo sauyi a jihar, yana mai cewa za su yi aiki tare domin “ceto Osun daga gwamnatin da ake ganin ba ta yi abin da ya dace ba.”
A nasa jawabin, shugaban Directorate of Youth, Students and Civil Society na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na Osun, Ayodele Asalu, ya ce taron ya ba matasa da ɗalibai damar jin tsare-tsaren Oyebamiji kai tsaye.
Ya ce matasan na son sanin yadda gwamnatin Oyebamiji za ta magance matsalolin ilimi da rashin aikin yi, tare da samar da damarmaki ga ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da ƙwararru.
Zaɓen gwamnan Jihar Osun zai gudana ne a ranar 15 ga Agusta, 2026, inda jam’iyyu 14 suka samu damar shiga takarar a cewar bayanan da a
ka bayar.
