Kasashen Algeria da Morocco sun samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA da za a gudanar a Brazil a shekarar 2027.
Algeria ta samu wannan nasara ne a karon farko a tarihinta, bayan da ta doke Côte d’Ivoire da ci 2-1, bayan da aka fara cin mata kwallo.
Ita ma Morocco ta samu tikitin bayan ta doke South Africa da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da ƙarshe na gasar Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON).
Samun gurbin zuwa wasan kusa da na ƙarshe na WAFCON ya ba ƙasashen biyu damar samun tikitin kai tsaye zuwa gasar cin kofin duniya ta 2027, bisa ƙa’idojin gasar.
Za a samu ƙarin ƙasashen Afirka biyu da za su wakilci nahiyar a gasar bayan kammala sauran wasannin daf da na kusa da ƙarshe.
A ranar Lahadi, Cameroon za ta kara da Nigeria, yayin da Malawi za ta kara da Ghana, inda waɗanda suka yi nasara za su samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya kai tsaye.
A gefe guda, Côte d’Ivoire da South Africa har yanzu suna da damar samun tikitin ta hanyar FIFA Play-Off Tournament.
Za a gudanar da gasar FIFA Women’s World Cup 2027 a Brazil.
