Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano sun ceto wani ma’aikaci mai suna Sadiq Ahmad da ransa bayan wata katanga ta rufta kansa yayin aikin rushe wani gini a Kofar Mata Zango, cikin Karamar Hukumar Kano Municipal.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 8:49 na safiyar Lahadi, inda nan take suka tura tawagar ceto zuwa wurin.
Rahotanni sun ce yayin da ake rushe wani gida mai girman kusan kafa 30 × 20, katangar ta kife ba zato ba tsammani, inda ta danne ma’aikacin yayin da yake kokarin tserewa.
Jami’an kashe gobarar sun samu nasarar ceto shi da ransa, sannan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin samun kulawar likitoci.
Hukumar ta ce tana ci gaba da binciken musabbabin rushewar katangar, tare da jan hankalin masu gine-gine da masu rushe gine-gine su kiyaye matakan tsaro domin kauce wa irin wannan hatsari a nan gaba.
