Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace da Etihad Airways sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin fadada zirga-zirgar fasinjoji tsakanin Najeriya da kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Yarjejeniyar za ta bai wa fasinjoji damar amfani da tikiti guda wajen tafiya zuwa garuruwa sama da 20, ciki har da Abuja, Kano, Fatakwal, Enugu, Benin, Owerri, Warri, Asaba, Abidjan, Dakar, Banjul, Monrovia, Freetown, Douala da sauran birane.
Kamfanonin sun bayyana cewa yarjejeniyar za ta kara saukaka zirga-zirga tsakanin Najeriya da Abu Dhabi, tare da bude karin damar kasuwanci da tafiye-tafiye ga matafiya.
Jami’in kasuwanci na Etihad Airways, Arik De, ya ce Najeriya na da muhimmanci a shirin fadada ayyukan kamfanin a nahiyar Afirka, yayin da jami’in kasuwanci na Air Peace, Nowel Ngala, ya ce hadin gwiwar zai samar wa kwastomomi karin zabin tafiye-tafiye cikin sauki.
Ana sa ran fasinjoji za su fara anfani da tsarin tikiti guda bayan yarjejeniyar ta fara aiki a hukumance, lamarin da zai kara inganta harkokin sufurin jiragen sama tsakanin Afirka da Hadaddiyar Daular Larabawa.
