Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta kara karfafa hadin gwiwa da Gwamnatin Jihar Kogi domin inganta shirye-shiryen tunkarar ambaliyar ruwa da kuma gaggauta daukar matakan ceto yayin damina.
Hakan ya biyo bayan ganawar da Shugaban Ofishin NEMA na Abuja, Zakari Abubakar, ya yi da Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Salifu Oyibo, a Lokoja.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin kara inganta shirin dakile bala’o’i, yada gargadin wuri, da kuma kare al’ummomin da ke cikin hadarin ambaliyar ruwa.
Zakari Abubakar ya ce NEMA za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin kare rayuka, dukiyoyi da muhimman ababen more rayuwa daga illar ambaliya.
A nasa bangaren, Mataimakin Gwamna Salifu Oyibo ya yabawa NEMA bisa irin goyon bayan da take bai wa jihar ta fuskar shirye-shiryen tunkarar ambaliya, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Kogi za ta ci gaba da aiki tare da hukumar domin rage illar ambaliyar ruwa a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa Jihar Kogi na daga cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci barazanar ambaliyar ruwa a bana, saboda matsayinta a mahadar kogunan Neja da Binuwe.
