Gwamnatin Tarayya ta rage kudin tantancewa da tsara matsayin littattafan karatu karkashin National Textbook Ranking System, tare da umartar a mayar wa masu wallafa littattafan da suka biya tsohon farashin karin kudin da suka biya.
Hukumar NERDC ta sanar da cewa an rage kudin tantance shafi daga N2,000 zuwa N1,500, yayin da kudin tsara matsayin kowane littafi ya sauka daga N1 miliyan zuwa N750,000.
Hukumar ta ce masu wallafa littattafan da suka riga suka biya tsohon farashi za a mayar musu da karin kudin, yayin da za a sanar da yadda za a gudanar da biyan kudin nan gaba.
Sabbin kudaden sun fara aiki nan take, kuma an bukaci dukkan masu wallafa littattafai da marubuta su bi sabon tsarin wajen gabatar da littattafansu domin tantancewa.
Daga Satumban 2026, gwamnati ta ce littattafan da ba su samu tantancewa da matsayi daga NERDC ba ba za a amince da amfani da su a makarantun Najeriya ba.
Ma’aikatar Ilimi ta bayyana cewa wannan tsari na daga cikin sauye-sauyen da aka bullo da su domin tabbatar da ingancin littattafan da ake amfani da su wajen koyarwa a makarantun fadin kasar.
