Kamfanin APM Terminals Nigeria ya yi kira ga gwamnatin Najeriya, kamfanoni masu zaman kansu, masu zuba jari da hukumomin raya ƙasa da su gaggauta samar da ababen more rayuwa masu kare muhalli a tashoshin jiragen ruwa, domin rage fitar da hayakin carbon da kuma ƙarfafa matsayin Najeriya a harkokin kasuwancin duniya.
Kamfanin ya ce Najeriya na buƙatar wuce matakin tsara manufofi zuwa aiwatar da ayyukan da za su iya jawo jarin dogon lokaci, tare da samar da fa’idodin tattalin arziki da muhalli da za a iya auna su.
Shugaban APM Terminals Nigeria, Frederik Klinke, ne ya yi wannan kira a taron koli na biyu na Decarbonizing Infrastructure in Nigeria (DIN) da aka gudanar a Abuja, mai taken “De-risking Green Infrastructure Investments: From Policy Architecture to Bankable Projects.”
Klinke ya ce duk da ci gaban da Najeriya ta samu wajen gyaran harkokin ruwa da kuma matakan kare muhalli, lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan ayyukan da za su samar da sakamako kai tsaye.
Ya ce manufofi da tsare-tsare kaɗai ba za su rage hayakin da ke gurɓata muhalli ba, sai an mayar da su zuwa ayyukan da za a iya aiwatarwa da samun jari.
Muhimmancin Rage Hayakin Carbon
Klinke ya bayyana cewa harkokin safarar kayayyaki ta teku na da muhimmiyar rawa a kasuwancin duniya, saboda fiye da kashi 80 cikin 100 na cinikayyar duniya bisa nauyin kaya na gudana ta teku.
Saboda haka, ya ce rage hayakin carbon a harkar safarar ruwa na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin kare muhalli tare da tabbatar da cewa Najeriya ba ta rasa damar yin gogayya a kasuwancin duniya.
Ya jero wasu abubuwan da suka kamata a samar domin sauƙaƙa sauyin zuwa tashoshin jiragen ruwa masu kare muhalli, ciki har da fayyace dokoki, tabbatar da shirye-shiryen ayyuka, samun ingantattun bayanan hayaki da kuma haɗa tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin mota, jirgin ƙasa da sauran hanyoyin jigilar kaya.
APM Ta Bayyana Hanyoyin Rage Hayaki
Babban jami’in gudanarwa na APM Terminals Nigeria, Koen De Backker, ya ce tashoshin jiragen ruwa da wuraren ajiye kaya na da muhimmiyar rawa wajen sauya harkokin sufuri zuwa tsarin da ya fi kare muhalli.
Ya ce rage hayaki zai fara ne da inganta yadda ake gudanar da ayyukan jigilar kaya, ta hanyar rage amfani da kayan aiki da man fetur, rage lokacin da manyan motoci ke jira, rage cunkoso da kuma inganta zirga-zirgar kaya.
Ya kuma bayyana cewa amfani da makamashi mai tsafta da fasahohin da ke fitar da ƙaramin hayaki na daga cikin hanyoyin da za su taimaka.
A cewarsa, rage hayaki a harkar safarar ruwa ba batun canza man fetur kawai ba ne, har ila yau yana da alaƙa da inganta yadda ake gudanar da ayyukan sufuri.
Gwamnati Ta Bukaci Ƙara Zuba Jari
Da yake wakiltar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya yi kira da a gaggauta yin gyare-gyaren manufofi tare da ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Hadejia ya ce ana kuma buƙatar sabbin hanyoyin raba haɗarin zuba jari domin jawo masu zuba jari daga cikin Najeriya da kuma ƙasashen waje zuwa ayyukan ababen more rayuwa masu kare muhalli.
Ya ce manufofin Najeriya na sauyin yanayi da bunƙasa ababen more rayuwa ba za su cimma nasara ba tare da ƙarin shigar kamfanoni masu zaman kansu, hukumomin samar da kuɗaɗen raya ƙasa da manyan masu zuba jari ba.
Shirin Wutar Lantarki A Tashoshin Jiragen Ruwa
Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ababen More Rayuwa na Jihohi, Musaddiq Adamu, ya ce taron DIN na da manufar rage tazarar da ke tsakanin ra’ayoyin samar da ababen more rayuwa masu kare muhalli da kuma aiwatar da ayyukan da za su iya jawo jari.
Ya ce tattaunawar da aka yi a taron farko ta taimaka wajen samun ci gaba a shirye-shiryen samar da wutar lantarki a tashoshin jiragen ruwa.
A cewarsa, tattaunawar da ta biyo bayan gabatarwar APM Terminals ta taimaka wajen samar da haɗin gwiwa tsakanin kamfanin da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) domin inganta amfani da wutar lantarki a ayyukan tashoshin jiragen ruwa, tare da sanya tashar Onne cikin misalan tashoshin jiragen ruwa masu kare muhalli a Najeriya.
APM Terminals ta kuma ce tana shirin, tare da haɗin gwiwar NPA, zuba jari a ababen samar da makamashi mai tsafta da kuma kayan aiki masu amfani da wutar lantarki a ayyukanta na Apapa da Onne.
Kamfanin ya ce shirin zai taimaka wajen inganta ayyukan tashoshin jiragen ruwa, rage hayakin da ke gurɓata muhalli, ƙara ƙarfin Najeriya a kasuwancin duniya da kuma tallafa wa manufofin ƙasar na kare muhalli.
Klinke ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su daina tsaya wa kan tattaunawa kawai, su mayar da hankali kan aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen rage hayaki da kuma samar da tattalin arziki mai ɗorewa.
