Kungiyar Barcelona ta nemi a sauya lokacin fara wasan ƙungiyar mata ta farko da za ta kara da Real Madrid a ranar Lahadi, daga ƙarfe 5:00 na yamma zuwa 7:00 na yamma, saboda barazanar ruwan sama mai ƙarfi da ambaliyar ruwa a yankin.
Barcelona ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce za a dakatar da dukkan ayyukan da ake gudanarwa a wuraren mallakar kungiyar daga ƙarfe 8:00 na dare ranar Asabar zuwa 2:00 na rana ranar Lahadi, bisa matakan da hukumomin da abin ya shafa suka shimfiɗa.
Dakatarwar ta shafi harkokin wasanni da atisaye, da kuma sauran shirye-shiryen al’adu, zamantakewa, nishaɗi da wasu abubuwan da aka tsara gudanarwa a wuraren kungiyar.
Sai dai har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe kan wasan mata da Real Madrid da aka shirya gudanarwa a Spotify Camp Nou ba.
Barcelona ta ce tana tattaunawa da hukumar Liga F da sauran hukumomin da ke da alhakin gasar domin tantance matakin da ya dace a ɗauka.
Kungiyar ta ce ta nemi a fara wasan da ƙarfe 7:00 na yamma, wato bayan sa’o’i biyu daga lokacin da aka tsara tun farko.
A cewar Barcelona, dage lokacin wasan zuwa gaba zai ba da ƙarin lokaci domin tabbatar da cewa filin wasan ya kasance cikin cikakken shiri tare da cika dukkan ƙa’idojin tsaro da ake buƙata.
Haka kuma, kungiyar ta ce sauya lokacin wasan zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar magoya baya da kuma shiga filin wasan, musamman saboda mawuyacin yanayin da ake fuskanta sakamakon ruwan sama.
Ana sa ran za a yanke hukunci na ƙarshe a safiyar Lahadi, bisa la’akari da yadda yanayin ruwan sama zai kasance da kuma umarnin hukumomin da abin ya shafa.
Barcelona ta ce za ta sanar da magoya baya da membobinta duk wani sabon bayani ta kafafen sadarwarta na hukuma.
