Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya na Najeriya, Festus Keyamo, ya tabbatar da cewa wani jirgin sojin sama ya yi hatsari a kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda, a jihar Ondo.
Keyamo ya bayyana cewa an gano tarkacen jirgin yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto.
Ya ce bayan samun bayanan farko, an tabbatar da cewa jirgin sojin ya yi hatsari ne a kusa da Naval Base da ke Igbokoda, inda ake ci gaba da kokarin gano halin da wadanda ke cikin jirgin suke ciki.
A cewar ministan, bayanan farko sun nuna cewa fasinja 25 da ma’aikatan jirgin 7 ne ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya faru.
Keyamo ya kuma bayyana cewa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya da kuma Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, NCAA, ba su da ikon kula ko tsara ayyukan jiragen soji.
Sai dai ministan ya ce ya tuntubi Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, tare da tabbatar masa da cewa ma’aikatar za ta bayar da cikakken hadin kai da taimako wajen aikin bincike da ceto da ake gudanarwa.
Ya kara da cewa za a fitar da karin bayanai game da hatsarin yayin da ake samun su.
