Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta tabbatar da cewa jirgin sojin da ya yi hatsari a yankin Igbokoda, jihar Ondo, a ranar Litinin, mallakin rundunar ne.
Rundunar ta bayyana cewa jirgin samfurin ATR-42 yana gudanar da wata tafiya ta yau da kullum daga Benin da ke jihar Edo zuwa Legas, lokacin da hatsarin ya afku a ranar 5 ga Oktoba, 2026.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, Ehimen Ejodame, ya ce rundunar ta fara aikin bincike da ceto nan take tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa da sauran hukumomin bayar da agajin gaggawa.
Ya ce jirgin yana kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas ne lokacin da hatsarin ya faru, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano tare da taimaka wa mutanen da ke cikin jirgin.
Rundunar Sojin Sama ta ce za ta ci gaba da bayar da cikakken bayani yayin da ake samun sabbin bayanai game da lamarin.
A baya, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun rasa hulɗa da jirgin mai lambar wutsiya NGR 931 da misalin ƙarfe 9:13 na safe.
Keyamo ya ce duk ƙoƙarin da aka yi na samun jirgin ta rediyo bai yi nasara ba, kafin daga bisani aka tabbatar da cewa jirgin ya yi hatsari a kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa an gano tarkacen jirgin, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto.
Bayanin farko da Keyamo ya bayar ya nuna cewa fasinja 25 da ma’aikatan jirgin bakwai ne ke cikin jirgin, wato jimillar mutane 32.
Sai dai NAF ba ta bayyana adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba, sannan ba ta bayyana halin da mutanen da ke cikin jirgin suke ciki ba.
Keyamo ya kuma jaddada cewa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya, NCAA, ba su da ikon tsara ko kula da jiragen soji.
Ya ce ya tuntubi Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, tare da tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ba rundunar cikakken haɗin kai da taimako wajen ayyukan bincike da ceto.
