Fitaccen dan wasan tennis na Spain, Carlos Alcaraz, ya lashe gasar Japan Open a karon farko tun bayan dawowarsa daga jinyar rauni da ta dauki tsawon watanni hudu.
Alcaraz, wanda shi ne na daya a jerin wadanda aka yi wa matsayi a gasar kuma mai rike da kambun gasar, ya doke dan wasan Czech Republic, Jiri Lehecka, da ci 7-6 (7/4), 6-4 a wasan karshe da aka gudanar a Tokyo ranar Talata.
Wannan ce kofin farko da Alcaraz ya lashe tun bayan gasar Qatar Open a watan Fabrairu, bayan ya shafe kusan watanni hudu yana jinya sakamakon raunin wuyan hannu.
Gasar Japan Open ita ce gasa ta uku da Alcaraz ya fafata tun bayan dawowarsa, bayan ya kai matakin daf da kusa da wasan karshe a US Open, sannan ya buga gasar Laver Cup.
Alcaraz ya bayyana cewa lokacin da yake jinya, tunani marasa dadi sun rika zuwa masa, musamman kan ko zai iya dawowa cikin koshin lafiya da kuma ko zai sake kasancewa a matakin da yake a baya.
Sai dai ya ce shi da tawagarsa sun kasance da yakinin cewa zai dawo cikin koshin lafiya sosai.
Wannan nasara ta kasance kofinsa na uku a shekarar 2026, yayin da kuma ta kai adadin kofunan da ya lashe a rayuwarsa ta kwallon tennis zuwa 27.
Alcaraz ya fuskanci kalubale daga Lehecka, wanda yake matsayi na 19 a duniya. Dan wasan Czech ya fara wasan da karfi inda ya karya hidimar Alcaraz tun da farko.
Sai dai Alcaraz ya dawo ya rama, kafin daga bisani ya yi amfani da kwarewarsa wajen lashe set din farko ta hanyar tiebreak.
A set na biyu ma Lehecka ya ci gaba da ba Alcaraz wahala, amma dan wasan Spain ya samu damar karya hidimarsa a tsakiyar set din, sannan ya kare wasan ba tare da wata matsala ba.
Nasarar ta zo ne sa’o’i kadan bayan dan wasan da ke matsayi na daya a duniya, Jannik Sinner, ya sanar da kawo karshen kakarsa da wuri saboda ci gaba da fama da raunin gwiwa.
Ana sa ran Alcaraz zai koma fafatawa a gasar Shanghai Masters, wadda za ta fara ranar Laraba.
