Masana kiwon lafiya a Najeriya da sauran kasashen Afirka sun yi kira da a dauki matakin gaggawa domin shawo kan matsalar cutar sickle cell, wacce ke kara yaduwa musamman a yankin Saharar Afirka.
An yi wannan kiran ne a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Abuja (Yakubu Gowon University), inda aka tattauna kan bincike da inganta hanyoyin kula da masu cutar sickle cell.
Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Hakeem Fawehinmi, ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin kasashen da ke da mafi yawan masu dauke da cutar, inda yake cewa ana haifar da yara kusan 150,000 a duk shekara da cutar. Ya ce yawancin wadannan yara na fuskantar wahalhalu kamar ciwo mai tsanani, rashin kudi, da karancin kulawa ta lafiya.
Ya jaddada cewa binciken da aka gudanar a karkashin shirin PACTS cikin shekaru hudu da suka gabata ya nuna hanyoyin da za su iya inganta rayuwar marasa lafiya idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.
Ya ce dole ne a wuce matakin magana kawai zuwa aiwatar da shawarwari domin rage matsalar.
Haka kuma, Bursar na jami’ar, Shiva M’ovul-Kondoun, ya ba da labarin yadda cutar ta shafi rayuwarsa, inda ya ce ya rasa ‘yan uwansa shida kafin su kai shekaru 30 sakamakon cutar. Ya bayyana wannan a matsayin abin bakin ciki da ke nuna yadda rashin kulawa ke jawo asara mai yawa.
Shi ma, Prof. Imelda Bates daga Liverpool School of Tropical Medicine, ta bayyana cewa shirin PACTS na mayar da hankali ne kan marasa lafiya, iyalansu da masu kula da su, domin gano matsalolinsu da samar da mafita mai dorewa a cikin al’umma.
Ta ce kusan 1 cikin 4 na ‘yan Najeriya na dauke da kwayar cutar sickle cell, yayin da kusan 1.5 zuwa 2% na al’umma ke dauke da cutar kai tsaye, wanda ke nuna cewa cutar ta zama babbar matsala ta kiwon lafiya.
A nata bangaren, Daraktar cibiyar a Najeriya, Prof. Obiageli Nnodu, ta bayyana cewa ana gudanar da bincike a asibitoci shida a FCT, inda ake duba yadda ake bin ka’idojin kula da marasa lafiya kamar amfani da magunguna da transfusion na jini.
Ta kuma ce akwai matsalar tsoro da kunyatarwa (stigma) a cikin al’umma da ke hana iyaye kai ‘ya’yansu asibiti da wuri.
