Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta fuskantar rikici mai tsanani a jihar, duk da yawan masu neman tikitin takarar gwamna gabanin zaben da ke tafe.
Yuguda ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi a gidan talabijin na ARISE, inda ya ce rashin cimma matsaya kan dan takara ta hanyar sulhu bai kamata a dauke shi a matsayin rashin hadin kai ba.
Ya ce jam’iyyar ta kafa kwamiti domin tattaunawa da duk masu neman takara domin kokarin cimma matsaya ta sulhu.
A cewarsa, idan sulhun bai yi nasara ba, APC za ta koma tsarin “Option A4” (zaben fitar da gwani kai tsaye) domin zaben dan takara.
Yuguda ya kuma jaddada cewa a matsayinsa na dattijo a jam’iyyar, ba zai goyi bayan wani takara kai tsaye ba, yana mai cewa dukkan masu neman takara suna da kima a idonsa.
A bangaren mulkin jihar Bauchi, tsohon gwamnan ya ce gwamnatin sa ta taba magance manyan kalubale kamar rashin isassun asibitoci da kuma yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya kuma bayyana cewa jihar yanzu tana samun kudin shiga fiye da lokacin da yake mulki, amma ya ce har yanzu ana iya yin fiye da haka idan an samu shugabanci nagari.
Yuguda ya kara da cewa batun rabon mulki (zoning) yana da muhimmanci, amma a siyasa galibi ana duba yawan kuri’u da karfin jam’iyya wajen cin zabe.
