Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) ta yi kakkausar suka kan rahotannin da ke nuna karuwar rikicin siyasa da tashin hankali a yankunan Ideato North da Ideato South a Jihar Imo.
Kungiyar ta ce ana samun rahotannin hare-hare, tsoratarwa da kuma hana ‘yan adawa gudanar da ayyukansu na siyasa, inda ta zargi wasu mutane da ake zargin suna da alaka da gwamnati da jami’an tsaro da hannu a lamarin.
HURIWA ta bayyana cewa abin da ke faruwa a Imo ya zarce rikicin siyasa na yau da kullum, tana mai cewa “yana nuna koma-baya ga dimokuradiyya da take hakkin jama’a.”
Kungiyar ta bukaci Gwamna Hope Uzodimma da ya dauki matakin gaggawa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da ‘yancin siyasa ga kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ba.
Haka kuma, HURIWA ta zargi cewa ana kai hare-hare kan magoya bayan wani dan majalisar wakilai, Ikenga Imo Ugochinyere, tana mai cewa ana amfani da ‘yan daba da sunan kungiyoyin tsaro wajen tarwatsa tarurrukan siyasa.
Kungiyar ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya yana tabbatar da ‘yancin taro, bayyana ra’ayi da shiga siyasa, don haka duk wani mataki na hana wadannan hakkoki “ya sabawa doka.”
HURIWA ta kuma bukaci Babban Sufeton ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi kan zargin cin zarafin ‘yan Adam da ake yi a sashen ‘yan sanda na Tiger Base a Owerri.
