Kamfanin Transmission Company of Nigeria (TCN) ya sanar da cewa wasu al’ummomi a jihar Delta za su fuskanci katsewar wutar lantarki sakamakon ci gaba da aikin gyaran tashar wutar Delta 132/33kV.
A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, ya ce aikin gyaran ya fara ne tun ranar 4 ga Yuni kuma zai ci gaba kullum daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 5:00 na yamma har zuwa ranar 16 ga Yuni, 2026.
TCN ta bayyana cewa ana gudanar da aikin ne domin haɗa sabuwar na’urar bus coupler circuit breaker da kuma gyaran wasu isolators guda biyar da ke kan babban layin rarraba wuta.
Kamfanin ya ce wasu layukan wutar lantarki na 33kV da ke samun wuta daga tashoshin Effurun da Delta 132/33kV za su kasance a kashe yayin gudanar da aikin.
Daga cikin wuraren da abin zai shafa akwai Effurun, Warri, Sapele, Osubi, PTI, PMSL, Refinery I da II, Enerhen, Isoko/Kwale, Otovwodo/Patani, Ughelli/Shell, Agbarho/Eku, Aladja, Imoniyame da Beta Glass.
Sai dai TCN ta tabbatar wa mazauna yankunan da ‘yan kasuwa cewa za a dawo da wutar lantarki a ƙarshen kowace rana bayan kammala aikin gyaran.
Kamfanin ya kuma ba da haƙuri ga jama’a kan duk wata matsala da katsewar wutar za ta haifar yayin gudanar da aikin.
