Hukumar ‘Yansanda ta Jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mambobi hudu na NYSC da kuma wani soja a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Yola–Mubi.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 1:50 na rana a yankin Narehi da ke Karamar Hukumar Girei/Song.
A cewar kakakin ‘yan sanda na jihar, SP Suleiman Nguroje, hatsarin ya shafi motar sojoji (gun truck) da ke tafiya daga Gombi zuwa Yola da kuma motar Hummer bus da ke dauke da fasinjoji biyar daga Yola zuwa Mubi.
Binciken farko ya nuna cewa motocin biyu sun yi taho-mu-gama ne, lamarin da ya sa motar fasinja ta kife tare da kama da wuta.
Dukkan fasinjojin motar biyar sun kone kurmus a wurin.
Rahoton ya tabbatar cewa hudu daga cikin wadanda suka rasu ‘yan NYSC ne masu hidimar kasa a Jihar Adamawa. Sun hada da Suleiman Juliet (mace) da Usman Shuaibu (namiji), dukkaninsu ‘yan Jihar Kaduna, yayin da sauran biyu ba a kammala tantance su ba.
Haka kuma an tabbatar da mutuwar wani soja da ke cikin motar sojojin.
An kai gawarwakin wadanda suka rasu Asibitin Kwararru na Yola domin ajiya da tantancewa.
Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, Kabir Hassan, ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, hukumar NYSC da Rundunar Sojojin Najeriya.
