Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC ta Kasa, Dr. Mary Alile Idele, ta bayyana cewa sabuwar kungiyar Tinubu Torchbearers (TTB) za ta zama dandali na wayar da kai a matakin kasa, tara jama’a, ilimantar da masu kada kuri’a da kuma karfafa hulda da ‘yan kasa domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
Ta yi wannan bayani ne a wajen kaddamar da kungiyar da aka gudanar a State House Banquet Hall da ke Abuja.
A cewarta, Tinubu Torchbearers wata kungiyar ce da aka gina daga tushe (grassroots) wacce ke da tsari a dukkan kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Ta ce:
“TTB kungiya ce da aka kafa domin zama hanyar wayar da kai, tara jama’a, ilimantar da masu zabe da kuma karfafa hulda da ‘yan kasa domin tallafa wa shirin Renewed Hope Agenda na Shugaban Kasa.”
Alile ta ce tsarin kungiyar a fadin kasa zai taimaka wajen isar da nasarorin gwamnati ga jama’a da kuma karfafa hadin kan ‘yan kasa wajen shiga harkokin mulki.
Ta kuma yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda yake gudanar da mulki, tana mai cewa gyare-gyaren tattalin arziki, bunkasa ababen more rayuwa, da tsare-tsaren tallafin jama’a na daga cikin abubuwan da ke nuna jajircewarsa.
Haka kuma ta jinjinawa Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, kan rawar da shirin Renewed Hope Initiative ke takawa wajen tallafa wa mata, matasa, nakasassu da marasa galihu.
A cewarta, shirin ya zama ginshiki na kawo tallafi kai tsaye ga al’umma ta fuskar ilimi, lafiya da bunkasa tattalin arziki.
Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu na aiwatar da sauye-sauye masu ma’ana ga rayuwar mata da yara da iyalai.
Ta ce an samar da sabbin tsare-tsare na kare yara, yaki da auren yara kanana da kuma magance cin zarafin yara a kasar nan.
Ta kuma ce an amince da shirin bayar da tallafin kudi ga yara da za a aiwatar tare da jihohi da UNICEF da sauran abokan hulda.
Haka kuma ta bayyana cewa an fara aiwatar da manufar ba mata ‘yan kasuwa damar samun kwangilolin gwamnati domin karfafa tattalin arzikin mata.
Sauran masu magana a taron sun bayyana cewa kungiyar Tinubu Torchbearers za ta kara karfafa goyon baya ga gwamnatin Tinubu tare da inganta hadin kan kasa da ci gaban al’umma.
